Philippians 2

Koyi Tawaliʼun Kiristi

1In kuna da wata ƙarfafawa daga tarayya da Kiristi, in da wata taʼaziyya daga ƙaunarsa, in da wani zumunci da Ruhu, in da juyayi da tausayi, 2to, sai ku sa farin cikina yǎ zama cikakke ta wurin kasance da hali ɗaya, kuna ƙauna ɗaya, kuna zama ɗaya cikin ruhu da kuma manufa. 3Kada ku yi kome da sonkai ko girmankai, sai dai cikin tawaliʼu, ku ɗauki waɗansu sun fi ku. 4Bai kamata kowannenku yǎ kula da shaʼanin kansa kawai ba, sai dai yǎ kula da shaʼanin waɗansu ma.

5Ya kamata haleyanku su zama kamar na Kiristi Yesu:

6Wanda, ko da yake cikin ainihin surar Allah yake,
bai mai da daidaitakansa nan da Allah wani abin riƙewa kam-kam ba,
7amma ya mai da kansa ba kome ba,
yana ɗaukan ainihin surar bawa,
aka yi shi cikin siffar mutum.
8Aka kuma same shi a kamannin mutum,
ya ƙasƙantar da kansa
ya kuma zama mai biyayya wadda ta kai shi har mutuwa-mutuwar ma ta gicciye!
9Saboda haka Allah ya ɗaukaka shi zuwa mafificin wuri
ya kuma ba shi sunan da ya fi dukan sunaye,
10don a sunan Yesu kowace gwiwa za ta durƙusa,
a sama da a ƙasa da kuma a ƙarƙashin ƙasa,
11kowane harshe kuma yǎ furta cewa Yesu Kiristi Ubangiji ne,
don ɗaukakar Allah Uba.

Haskaka kamar Taurari

12Saboda haka, ya abokaina ƙaunatattu, kamar yadda kullum kuke biyayya-ba kawai saʼad da ina nan ba, amma yanzu da ba na nan tare da ku-ku ci gaba da yin ayyukan cetonku da tsoro da kuma rawan jiki, 13gama Allah ne yake aiki a cikinku, don ku nufa ku kuma aikata bisa ga nufinsa mai kyau.

14Ku yi kome ba tare da gunaguni ko gardama ba, 15don ku zama marasa abin zargi, sahihai ʼyaʼyan Allah, waɗanda ba su da laifi, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya 16kuna kuwa cin gaba da riƙe maganar rai-domin in yi taƙama a ranar Kiristi cewa ban yi gudu ko fama a banza ba. 17Amma ko da ana tsiyaye jinina kamar hadaya ta sha a kan hadaya da kuma hidimar da take fitowa daga bangaskiyarku, ina murna ina kuma farin ciki da ku duka. 18Haka ma ya kamata ku yi murna ku kuma yi farin ciki tare da ni.

Timoti da Afaforiditus

19Ina sa rai a cikin Ubangiji Yesu cewa zan aika da Timoti zuwa gare ku ba da daɗewa ba, don ni ma in ji daɗi saʼad da na ji labarinku. 20Ba ni da wani kamarsa, wanda yake da ainihin shaʼawa a zaman lafiyarku. 21Gama kowa yana lura da alʼamuran kansa ne kawai, ba na Kiristi Yesu ba. 22Amma, ai, kun san darajar Timoti yadda muka yi bautar bishara tare, kamar ɗa da mahaifinsa. 23Saboda haka, ina sa rai, in aike shi da zarar na ga yadda abubuwa suke a nan. 24Ni kuma ina da tabbaci a cikin Ubangiji cewa zan zo ba da daɗewa ba.

25Amma ina gani ya dace in aika da Afaforiditus, ɗanʼuwana, abokin aikina da kuma abokin famana, wanda kuma yake ɗan saƙonku, wanda kuka aika domin yǎ biya mini bukatuna. 26Gama yana marmarin ganinku duka ya kuma damu domin kun ji cewa ya yi rashin lafiya. 27Ba shakka ya yi rashin lafiya, har ya kusa mutuwa. Amma Allah ya nuna masa jinƙai, ba shi kaɗai ba amma har da ni ma, don yǎ rage mini baƙin ciki kan baƙin ciki. 28Saboda haka na yi niyya ƙwarai in aike shi wurinku, don saʼad da kuka sāke ganinsa za ku yi murna, ni kuma in rage damuwa. 29Ku marabce shi cikin Ubangiji da farin ciki mai yawa, ku kuma girmama mutane irinsa, 30domin ya kusa yǎ mutu saboda aikin Kiristi, ya yi kasai da ransa don yǎ cikasa taimakon da ba ku iya yi mini ba.

Copyright information for HauSRK